1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Ban Ki Moon a Libanon

March 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuOl

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Ban ki Moon, na ci gaba da ziyara aikin a ƙasar Libanon.

Ya gana a birnin Beyruth inda ya gana da hukumomin a game da batun kissan tsofan, praminista Rafik Hariri a shekara ta 2005 da kuma yarjejeniyar da Majalisar Ɗinkin Dunia ta rattaba hannu kanta, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin da Isra´ila da Hizbullahi.

Ban Ki Moon, ya bayana buƙatar aiki sau da ƙafa, da wannan yarjejniya, da kuma mutuntunta kotun mussamman da aka girka, domin shari´ar mutanen da ake tuhuma da lefin kissan Rafik Hariri.

Wannan ziyara na wakana, a lokacin da kasar Libanon ta tsunduma cikin ƙiƙi-ƙaƘƙar siyasa, wadda ita ce irin ta mafi muni, tun shekara ta 1990

Rikicin ya samo assuli tun bayan da ministoci 6, masu goyan bayan Syria, su ka yi murabus daga gwamnati, a matasyin maida martani, ga girka kotun ƙasa da ƙasa wada zata gudanar da shari´ar mutuwar Hariri.