1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Charles Konnan banny a ƙasar France

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv27

A cigaban da ziyaran aikin da ya kai a ƙasar France, Praministan ƙasar Cote d´ivoire Charles Konnan Banny, ya yi taro manema labarai a yau laraba.

Charles Konnan Banny, ya bayyana burin sa, na shirya zaɓe a cikin wa´adin da a ka tanada.

Saidai, idan buƙatar ƙarin lokaci ta taso, zai tantana da ɓangarori daban-daban, domin tsaida ranar, da zata samu amincewar kowa.

A ɗaya hannun Charles Konnan Banny ,ya buƙaci rundunonin France, da na Majalisar Ɗinkin Dunia, su ci gaba da zama a Cote D´ivoire, har ƙarshen rikicin tawaye a ƙasar.

Praministan, ya gana da shugaba Jaques Chirac, da ministocin kuɗi na hulɗoɗi da ƙetare, da kuma na tsaro, kazalika, ya tantana da ƙungiyar shugabanin kampanoni da masana´antu.

Wannan ziyara na gudana a yayin da ake fuskantar wata sabuwar taƙƙadama a Cote d´Ivoire.

A yau laraba ne, a ka shirya ganawa, tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati, amma a ka dage wannan taro dalilin da rashin halartar yan rawayen.