1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Charles Konnan Banny a Bruxelles

Yahouza SadissouMay 3, 2006

Praministan ƙasar Cote d´Ivoire Charles Konnan Banny ya kai ziyara cibiyar gamayyar turai dake Bruxelles

https://p.dw.com/p/Bu0M

Praministan ƙasar Cote d´ivoire Charles Konnan Banny, na ci gaba da ziyara aiki a cibiyar ƙungiyar gamayyar turai da ke birnin Brussels na Belgium.

A matakin farko na wannan ziyara, Praminista Charles Konnan Banny, ya gabatar da jawabi gaban komitin tattali da bada agaji na Ƙungiyar gamayya turai.

Ya yi anfani da wannan dama, domin miƙa kira da babbar murya, ga EU, ta ƙara ba shi ƙarfin gwiwa, don nasara kuɓuto Cote d´Ivoire, daga halin da ta ke ciki a yanzu.

Ƙasar, ta kama hanyar hita daga rikicin tawaye, da rigingimun siyasa, to amma hakan ba zai samu ba, sai da taimako, da haɗin kan kungiyar tarayya turai, inji Charles Konnan Banny.

Praministan ya bayyana bukatar wannan taimako, ta fannin aiwatar da dokokin da ke ƙunshe cikin taswira zaman lahia, da majalisar Ɗinkin Dunia ta gabatar, kuma ɓangarori daban-daban masu gaba da juna, su ka amince da ita.

Konnan Banny, ya hau muƙamin Praministan riƙwan ƙwarya, tun watan Desember da ya gabata, babban yaunin da ya rataya a wuyen sa, ya haɗa da shirya zaɓɓuka, daban-daban kamin watan oktober mai zuwa, da kuma kwance makamen yan tawaye da na ƙungiyoyin sakai, masu nuna goyan baya ga shugaban ƙasa Lauran Bagbo.

Ya ƙara jaddadawa ƙungiyar gamayya turai, mahimancin cimma nasara kwance ɗamaru, da kuma samar da ayukan yi, ga dakarun da za su ajje makamai.

A yammacin jiya, ya tantana da komishinan tattalin arzikin EU, Louis Michel a danganer da wannan batutuwa.

A yayin da Charles Konnan Banny, ke ci gaba da ziyara a Berussels, wata tawagar assusun bada lamani na dunia, ta kai randagi ƙasar Cote d´ivoire.

Wannan shine karon farko, da IMF, ya aika wakilai kasar, tun hawan Charles Konnan banny a kan karagar mulki.

A lokacin da Praministan,ya kai ziyara a cibiyar IMF,a watan Maris da ya gabata, shugaban Rodrigo Rato, ya alkawarta masa cewar IMF a shire ya ke, ya sake ƙulla hulɗoɗi da Cote D´ivoire.

Ziyara tawagar assusun bada lamani zata ɗauki tsawan kwanaki 14, domin ƙalailaice halin da ake ciki, ta fannin tatalin arzikin Ivory Coast, mussamman a ɓangaren Koko, da Cafe, wanda akan su ƙasar ta yi suna a dunia, saidai wannan albarkatu, a hakin da ake ciki, na fuskantar taɓarɓarewa a sakamakon rikicin tawaye.