1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Christopher Hill a Asia

July 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bur5

Ƙasashen Amurika da Japon sun jaddada kira, ga hukumomin Korea ta Arewa, domin su koma tebrin shawarwari, a kan rikicin makaman nuklea, da makamai masu lizzami, da Korea ta Arewa, ta harba a makon da ya gabata.

Saidai ƙasashen 2, sun ce ba za su janye buƙatar su ba, ta neman hukumta Korea ta Arewa, a komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

A ziyara da ya kai, yankin Asia, wakilin mussamman na Amurika Christopher Hill, ya ce muddun hukumomin Pyong Yang, su ka yi watsi da wannan kira, babu shakka za su gane kuren su.

A ɗaya wajen Christopher Hill, yayi kira ga Rasha da Chine da cewar lokaci yayi, na su cenza tunanin su, a kan goyan baya ido rufe da su ke baiwa Corea ta Arewa.

Ƙasashen 2, sun bayana aniyar hawa kujerea naƙi, a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, a game da hukucin da a ke bukatar ɗauka kan Corea ta Arewa.