1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice a gabas ta tsakiya

Yahouza S.MadobiJanuary 15, 2007

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice,na ci gaba da ziyara a yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/Btwd
Hoto: AP

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, na ci gaba da ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya, inda ɗaya bayan ɗaya, ta ziyarci ƙasashen Palestinu Isra´ila da Masar.

A matakin farko na wannan rangadi, irin sa, na 8 da Condoleesa Rice ta kai yankin gabas ta tsakiya, a tsawan shekaru 2, ta gana da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, inda su ka tantana batun samar da zaman lahia a wannan yanki da ke fama da tashe-tashen hankulla.

Rice ta alkawarta cewar gwanatin Amurika zata yi iya kokarin a yubnkurin shinfiɗa kwanciyar hankali a yankin, ta hanyar tantanawa cikin ruwan sanhi, tare da ɓangarori masu gaba da juna, da kuma ƙasashen dunia masu shiga tsakani.

„ Amurika na muradin lalubo hanyoyin cimma nasara cikin gaggawa, domin tabbatar da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya, tara da farfaɗo da taswira zaman lahia, da ɓangarorin 2, da kuma ƙasashen dunia su ka amince da ita“.

Condoleesa Rice ta jaddada wannan mataki a ganawar da ta yi sahiyar yau, da Praministan Isra´ila Ehud Olmert.

Ta yi kira ga hukumominn bani yahudu, su tallafawa Mahamud Abbas, a rikicin da ya haɗa shi, da ƙungiyar Hamas,da ke riƙe da ragamar gwamnatin Palestinu.

Jim kaɗan bayan wannan tantanawa, kakakin sakatariyar harakokin wajen Amurika, ya bada sanarwar shirya taro na musamman da zai haɗa Condoleesa Rice, Ehud Olmert, da Mahamud Abbas, nan da yan kwanaƙi masu zuwa, wanda a sakamakon sa, a ke sa ran cire tarnaƙin da ya hana ruwa gudu, a yunƙurin cimma burin da a ka sa gaba, na shinfiɗa zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.

Za a kiri wannan taro, bayan ganawar da za ta haɗa ƙasashe masu shiga tsakanin rikicin gabas ta tsakiya,a farkon watan februaru a birnin Washington na ƙasar Amurika.

Bayan Palestinu da Isra´ila Condoleesa Rice, ta sauka a ƙasar Masar, domin masanyar ra´ayi da shugaba Hosni Mubarack, da kuma Sakatare Janar da ƙungiyar gamayyar larabawa Amr Musa, a game da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Saidai a wani mataki na a magani kai na kaɓa, ziyara sakatariyar harakokin wajen Amurika, ta zo daidai lokacin da, Praministan Isra´ila, ya bada kwangilar gina wasu sabin matsugunan yahudawa a yankin Male Adumin mallakar Palestinu.

Hukumar Palestinawa ta yi tur da Allah wadai da wannan saban mataki, da ta danganta da tunƙa da walwala.

Kazalika, shugaban komitin ƙasar Isra´ila, mai adawa da mamayar Palestinu, ya bayyana rashin amincewa da wannan mamaya, ya kuma nunar da cewa matakin na matsayin tofin Allah tsine ga ziyara Condoleesa Rice.