1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice a Indonesia

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv59

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta fara ziyara aiki a ƙasar Indonesia.

Jim kaɗan, kamin ta sauka a Jakarta, babban birnin ƙasar, Rice, ta yaba nasarori da gwamnatin Indonesia ta samu, ta fannin shinfiɗa tsarin mulkin demokraɗiya, da kuma ƙoƙarin samar da zaman lahia, tsakanin gwamnatin, da yan tawayen Aceh, da na gabacinTimo.

A ganawar farko da ta yi da shugaban kasa Indonesia, Susilo Bambang Yudhoyono, sun yi mansanyar ra´ayoyi ,a game yanayin tsaro da zamankewa a nahiyar Asia, mussamna a kan batun yaƙi da ta´andanci, a Indonesia, ƙasa mafi yawan musulmi a dunia baki ɗaya.

Indonesia da Amurika, na hulɗoɗi ta fannin tsaro, da cinikaya da kuma taimakon raya ƙasa.