1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice a Jamus

December 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvHl

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condolisa Rice, ta fara ziyara a aiki a nahiyar turai.

Tun daren jiya, ta sauka a Berlin, babban birnin taraya Jamus, inda nan gaba a yau, za ta gana da shugabar gwamnati Angeler Merkel.

Wannan itace ganawa ta farko, tsakanin Rice da Angeller Merkel.

Jim kadan bayan zaben ta, a matsayin shugabar Gwamnati, Merkell ta bayyana burin ta na kulla dangata ta kut da kut tsakanin Jamus da Amurika.

Dan lokaci kadan, kamin ta fara wannan rangadi, Condolisa Rice, ta yi kira ga kasashen turai, da su matsa kaimi, wajen yaki da ta´adanci a dunia.

A tantanawar ta, da Angeller Merkell, za su masanyar ra´ayoyi, a game da mu´amila tsakanin Jamus da Amurika , da kuma manyan kalubale da dunia ke fuskanta a sassa daban daban.

Bayan Jamus, Sakatariyar harakokin wajen Amurika, zata ziyaraci kasashen Rumania da Ukraine, kazalika zata halarci taron kungiyar tsaro ta NATO, a birnin Brussels,a game da batun sirin da kafofin sadarwa su ka bankado, na cewar Amurika ta yi anfani da hilayen saukar jiragen samar wasu, daga kasashen turai a assurce,domin jigilar prisinoni, da ta ke zargi da ta´adanci.