1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Dick Cheney a Gabas ta tsakiya

May 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuLZ

A ci gaba da lalubo hanyoyin warware rikicin yankin gabas ta tsakiya, yau ne mataimakin shugaban ƙasar Amurika Dick Cheny, ya gana da shugaba Hosni Mubarak na ƙasar Masar.

Mahimman batutuwan da magabatan su ka tantana a kai, sun shaifi halin da ke ciki, a ƙasar Irak, dackuma katsa landa, da a cewar Amurika, Iran ke yi, a harakokin cikin gida na Irak.

Babban burin da Amurika ke buƙatar cimma shine, shawo kan ƙasashen larabawa, su bada haɗin kai, wajen warware sarƙƙaƙiyar rikicin Irak, tare da neman shawarwari, ta fannin kai ga sahihan matakai, na raba mulki, tare yan Sunni na wannan ƙasa.

Da dama daga manazartan harakokin addini, a Amurika, na kyauttata zaton, rikicin addini a ƙasar Irak, zai ciga ba rincaɓewa, ta la´akari da goyan baya da yan Sunni ke samu daga Saudi Arabia, a yayin da yan Schi´a, ke da ɗaurin gindi daga Iran.

A game da haka,kamin ganawa da shugaba Mubarack, saidai Dick Cheney,ya tantana da Sarki Abdallah na Saudi Arabia, sannan zai zarce gobe a ƙasar Jordan.