1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Ehud Olmert a turai

June 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuuK

Praministan ƙasar Isra´ila Ehud Olmert, ya fara ziyara aiki ta farko, a nahiyar turai, tun bayan da hau karagar mulki.

A matakin farko na wannan rangadi, zai gana nan gaba a yau, da takwaran sa na Britania Tonny Blair.

Sannan ranar laraba, ya haɗu da shugaban ƙasar France Jacques Chirac.

Babban burin wannan ziyara,, ya ta´alaƙa da yaɗa manufofin Isra´ila, na shata iyakoki, tsakanin ta da Palestinu, da kuma tantana batun rikici tsakanin ƙasashen 2.

Saidai ziyara na wakana, a yayin da rikicin, ya ɗau wani saban sallo, tun bayan harin da dakarun Isra´ila su ka kai hari,ranar juma´a da ta wuce, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Palestinawa 8 fara hulla.

Praminista Olmert,ya ƙudurci rusa yankunan Yahudawa yan kaka gida, da ke yamma ga kogin Jordan, tare da gina wasu sabin yankunan mamaye, a fadamun Jourdain matakin da ƙasashen turai su ka yi watsi da shi.

Idan ba a manta ba, ministan harakokin wajen ƙasar France,, Phillips Duzte Blazy, ya ziyaraci Isra´ila a watan mayu da ya gabata, inda ya bayyana matsayin ƙasar sa, na ƙin amincewa da batun.