1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Fraministan Isra'ila a ƙasar Girka

August 17, 2010

Benjamin Netanyahu na nemam ƙula hulɗa da ƙasar Girka

https://p.dw.com/p/Op8P
Benjamin NetanyahuHoto: AP

Friministan ƙasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana kyaukkyawan fatan cewa na ba da daɗewa za a koma ga yin shawarwarin gaba da gaba na wanzar da zaman lafiya tsakanin Palasɗinu da Isra'ila.

Netanyahu da ke magana a sa'ilin ziyara da ya kai a birnin Athens na ƙasar Girka, ya ce a shirye suke su je birnin alƙahira, da washinton domin tattauna butun shirin na zaman lafiya.

friministan na Isra'ila wanda ya fara ziyara a ƙasar Girka a jiya litinin na kokarin neman samu wata sabuwar hulɗa ne a yankin na mediteranien, bayan rashin jituwar da ta auku tsakanin Isra'ila da ƙasar Turkiya a watannin da suka gabata.

wannan dai ita ce ziyara ta farko da wani shugaban Isra'ilan ya ke yi a ƙasar Girka wacce ke da allaƙa dakuma hulɗa da ƙasashen larabawa.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu