1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Havier Solana a DRC

September 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bujq

Komishinan harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai Havier Solana, na ci gaba da tantanawa da ɓangarori daban-daban na siyasa a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.

Wannan itace ziyar farko, da ya kai a ƙasar, tun bayan zaɓɓuɓukan ƙarshen watan yuli da ya wuce, wanda a sakamakon su, arangama ta ɓarke, tsakanin magoya bayan Jean Pierre Bemba, da na Joseph kabila, yan takarar, da za su fafata, a zagaye na 2 na zaɓen shugaban ƙasa.

A ɗaya wajen Solana, ya gana da shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a birnin Kinshasa, da kuma shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta.

Komishinan harakokin wajen EU, ya bayana gamsuwa da tantanwar da yai , ya kuma tabbatar da cewa, nan bada jimawa ba, Joseph Kabila, da Jean Pierre Bemba, za su haɗu da juna, domin shirya matakan gudanar da zagaye na 2, na zaɓen shugaban ƙasa, cikin kwanciyar hankali da fahintar juna.