1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Hu Jin Tao a ƙasar Amurika

April 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1R

A yammacin jiya ne, shugaban ƙasar China Hu JinTao, ya sauka ƙasar Amurika, inda ya kai ziyara kwanaki 4.

Tun bayan hawan sa mulki , a shekara ta 2003, wannan shine karo na farko, da shugaban China, ya kai ziyara a fadar white House, domin ganawar ƙeƙe da ƙeƙe da shugaban Geores Bush.

Tawagogin 2, za su masanyar ra´ayoyi a game da harakokin saye da sayarwa, tsakanin China da Amurika, da kuma wasu batutuwa na diplomatia da na harakokin siyasar dunia.

Hu Jin Tao, ya yi ganawar farko da shugaban kampanin Microsoft , shaharraran mai kuɗin nan, na Amurika Bill Gates.

A yau, zai ci gaba da ganawa da shugabanin kampanoni, kamin ya haɗu da Georges Bush a gobe alhamis.

Masharahanta na nuni da cewar bayan harakokin saye da sayarwa, batun rikicin makaman nuklear ƙasar Iran, zai kasance sahun gaba, a ajendar tantanwa tsakanin shugabanin 2.