1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Hu JinTao a Afrika

April 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0j

Shugaban ƙasar China, Hu JinTao na ci gaba da ziyara a nahiyar Afrika.

Bayan Marroko inda ya ke a halin yanzu Hu JinTao, zai ziyaraci Nigeria da Kenya.

A birnin Rabat, inda ya gana da Sarki Mohamed na 6, sun rattaba hannu a kan yarjeniyoyi 7, tsakanin ƙasashen su.

Wannan yarjejeniyoyi, sun shafi saye da sayarwa, ta takin zamani, da kayan gina , da harakokin yawan buda ido,sannan da bincike, ta fannin kimiyya da Fassaha.

A halin yanzu, ƙasar China ,ta kwace harakokin kasuwa tsakanin Afrika ta turai, inda ako wace shekara a ke ƙara samun hauhawar hajojin China, a cikin wannan nahiya.

A yayin da ya ke hira da manema labarai ,Hu JinTao ya tabbatar da cewa, China a shire take, ta kara hulɗa, da Afrika, sannan a game da hare haren ta´adacin da su ka wakana jiya a Masar, ya kira ga kasashen dunia da su tashi tsaye tsayin daka, domin magance matsalolin ta´adanci a dunia.