1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Hugo Chavez a Iran

July 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuHL

Shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez, ya gana da Ayatollah Ali Khameni na Iran, albarkacin wata ziyara aikin da ya fara a ƙasar.

Magabatan 2, sun yi suka da kakkausar halshe, ga shugaba Georges Bush na Amurika, wanda Chavez ya danganta da sheɗani mai tada hasumi a dunia.

Kazalika sun ce, ƙasashen Iran da Venezuela, sun yanke shawara gama ƙarfi domin fuskantar barazanar Amurika.

Wannan ita ce ziyara ta 3, da Hugo Chazvez ya kai Iran, tun bayan da ka zaɓi Mahamud Ahmadinedjad a matsayin shugaban ƙasa.

Nan gaba ayau Chavez zai kammala wannan rangadi, bayan tawagogin 2 sun rattaba hannu a kan yarejeniyoyi daban-daban ta fannin saye da sayarwa.