1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jacques Chirac a Sin

October 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bueg

Shugaban ƙasar France Jacques Chirac ya fara ziyara aikin kwanaki a kasar Sin.

Wannan itace ziyara irinta ta 4 da Chirac ya kai akasar tunbayan hawan sa mulki a shekara ta 1995.

Tawagar shugaban France ta ƙunshi manyan shugabanin kampanoni da masan´atu, da za su gana da takwarortin su na China.

Mahimman batutuwan da Jacque Chirac zai tantana kann su da hukumomin China, sun haɗa da samun kwangilar gina wani layin dogo, tsakanin biranen Wuhan da Canton.

Bayan tantanawar share fage, gobe idan Allah ya kai mu,shugaba Chirac zai sadu da takwaran sa na China, Hu JinTao.