1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jan Egeland a kasar Cote D`Ivoire

Yahouza SadissouFebruary 15, 2006

Mataimakin Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Jan Egeland ya kai ziyara aiki a kasar Cote D`Ivoire.

https://p.dw.com/p/Bu1g
Hoto: AP

A yammacin jiya ne,Jan Egeland ya fara wannan ziyara ta kwanaki 3, inda zai gana da bangarori daban daban, na kasar Cote D´Ivoire masu gaba da juna, da kuma wakilan majalisar Dinkin Dunia da ke kasar.

A yau laraba Egeland yayi ganawar farko,da shugabanin rundunar majalisar Dinki dunia, dake shiga tsakani, da sauran kungiyoyi da ke wakiltar majalisar.

Kazalika, ya tantana da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a fannoni daban daban na rayuwa.

Gobe idan Alllah ya kai, mu zai ziyarci yankin Guiglo, da ke arewancin kasar, inda idan ba ku manta ba, a tsakiyar watan da ya gabata, gungun wasu matasa, dake goyan bayan shugaban Lauran Bagbo, su ka kai hari ga tawagar Majalisar Dinkin Dunia.

Bayan yankin Guiglo, Jan Egeland, zai yada zango a Bouake cibiyar yan tawaye, domin tantanawa da shugabanin wannan kungiya da ke rike da yankin, tun shekara ta 2002.

Ranar juma´a idan Allah ya kai mu, zai sadu da shugaban kasa, Lauran Bagbo, da Praminista Charles Konnan Banny, kamin ya halarci taron komitin shiga tsakanin rikicin Cote D´ivoire, a wani zama na mussaman.

Babban burin da Jan Egeland ke dauke da shi, a wannan ziyara, shine na bukatar bangarori daban daban da ke gaba da juna a wannan kasa, su cika alkawuran da su ka dauka, na kare hakkokin jama´a, wanda basu ci kasuwa ba, runfuna ke masu.

Sannan su ba kungiyoyin tallafi na kasa da kasa, damar shiga wuraren da su ke bukata, domin agazawa talakawa.

Bugu da kari, Jan Egeland ,na dauke da burin samun cikkaken bayani ,a game da inda aka kwana, ta fannin shirye shiryen zabe a watan oktober mai zuwa,da kuma maido da zaman lahia a kasar Cote D´Ivoire.

A nasa bangare Charles Ble Gude, shugaban gungun matasa masu goyan Lauran bagbo, wato les Jeunes Patriotes, kokuma matasa yan kishin kasa, a yammacin yau laraba, ya hido da wata sanarwa, inda ya yi hannun ka mai sansda ga komitin kasa da kasa na shiga tsakain a Cote D´Ivoire.

A cikin sanarwar, Charles Ble Gude, ya ja hankullan membobin wannan komiti, da su yi takatsantasan a taron da su gudanar ranar juma´a mai zuwa.

Ya yi masu barazana da cewa, kar su wuce makadi da rawa, a cikin shawarwarin da su gabatar.

Ya kasance wannan shawarwari ba za su sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba, a game da haka, kungiyar Jeunes Patrioteas na tsaye kan bakan ta inji Ble Gude.

Idan ba a manta ba,a tsakiyar watan Janairu da ya gabata, komitin shiga tsakanin na kasa da kasa, ya bayyana kin amincewa da hukunci da shugaba Lauran Bagbo, ya yanke na zarcewar Majalisar Dokoki, bayan wa`adin ta, ya kai karshe.

Wannan matsayi,da komitin ya dauka, ya hadasa zanga zangar kwanaki 4, inda matasa yan gani ka shenin Bagbo, su ka kai hare hare ga tawagogin majalisar Dinkin Dunia.

Wannan Komitin mai shiga tsakani, na kasa da kasa, ya kunshi wakiln Majalisar Dinkin Dunia, da na kungiyar Taraya Afrika da Kungiyar Gamaya Turai, da kungiyar kasashe masu anfani da halshen Farasanci wato OIT, sanan da wakilan bakin dunia, da assusun bada lamani.

Kazalika ,wannan komiti ya kunshi wakilan kasashen Afrika ta kudu, Benin, Niger, Ghana, Guniee, Nigeria , da wasu kasashen turai da su ka hada da Faransa da Britania da kuma kasar Amurika.