1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Javier Solana a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo

Yahouza SadissouMarch 20, 2006

Sakataren harakokin wajen EU Javier Solana,ya kammala ziyara aiki a Jamhuriya Demokaradiyar Kongo

https://p.dw.com/p/Bu16
Hoto: AP

Sakartaran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Javier Solana, ya kai ziyara aiki ta yini 2 a Jamhuriya Demokaraɗiyar Kongo.

Maƙasudin ziyara ta Javier Solana,dai, shine na gani da iddo, halin da a ke ciki a Jamhuriya Demokaraɗiyar Kongo, da kuma tsaida mattakan tura dakarun ƙungiyar gamayya turai, a wannan ƙasa da ke fama da tashe tashen hankulla.

Yuuni a rataya a kann wannan runduna na tabatar da tsaro a lokacin a zaɓen shugaban kasa da za a yi, a watan juni mai zuwa, wanda kuma shine irin sa na farko, tun fiye da shekaru 40 da su gabata.

Javier Solana, ya yiwannan rangadi, bisa buƙatar ministocin tsaro na ƙasashe membobin EU .

A watan desember da ya gabata Majalisar Ɗinkin Dunia, ta buƙaci ƙungfiyar gamayya turai, ta tura dakarun ta a yankin tsakiyar Afrika, mussamn a jamhuriya Demokarɗiyar Kongo domin tallafawa rundunar ƙasa da ƙasa, da har kawo yanzu ta kasa magance riginginmun tawayen da a ke fama da su.

A sakamakon wannan ziyara ta yini 2,Javier Solana, ya gana da shugaban ƙasa Lauran Kabila ,da ɓangarori daban daban masu gaba da juna, a ƙasar.

Kazalika, Solana ya tantanna da shugaban rundunar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Dunia, da ke birnin Kinshasa William Swing da shugaban hukumar zaɓe mai kanta Appolinaire Malu Malu.

Ya yi kira zuwa gare su, da babbar murya, a kann mahimancin shirya zaɓe cikin kwanciyar hankali a wannan kasa,domin girka sabuwar gwamnati.

Ƙungiyar gamayya turai, ta saka kuɗaɗe kimkanin Euro milion ɗari 8, a cikin ayyukan gwamnatin riƙwan ƙwarya a jamhuriya Demokaraɗiya Kongo.

Nan gaba a yau ne, Javier Solana zai gabatar da rahoton ziyara ta sa ga taron ministocin harakokin wajen EU, da a ka fara a birnin Brussels.

A ɗazunan kuma, mininistan harakokin tsaro, na Jamus Franz Josef Jung, ya bada labarin cewa, a birnin Postdam ne ,na ƙasar Jamus, za a girka sassanin rundunar da EU zata tura, a Jamhuriya Demokariyar Kongo, kuma ƙasar France zata jagoranci wannan runduna a birnin Kinshassa.

A jimilce, rundunar zata ƙunshi sojoji dubu ɗaya da ɗari 5 .

Jamus zata bada sojoji 500, haka zalika France, sai kuma Spain, Poland, Italia, Britania, Girka ,da Austriyya su haɗa sauran sojoji 500.