1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Koffi Annan a Cote d´Ivoire

July 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bure

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, na ci gaba da randagi a yankin yammacin Afrika.

Bayan Sierra Leone, Annan zai ziyaraci ƙasar Cote d´Ivoire gobe idan Allah ya kai mu, inda zai bitar halin da ake ciki a game da batun zaɓɓuɓukan da za a shirya, a shekara bana.

Wannan itace ziyara farko, da Annan zai kaiwa Cote d´Ivoire, tun bayan da ta rabu gida 2, a shekara ta 2002.

Koffi Annan, za shi wannan ziyara, tare da rakiyar shugaban ƙungiyar taraya Afrika Denis Sassu N Guesso, da shugaban ƙungiyar ECOWAS Tandja Mamadu, da shugaba Tabon Mbeki na Afrika ta kudu, da ke shiga tsakani a rikicin Ivory Coast, sai kuma shugaba Olesegun Obasanjo, na taraya Nigeria wanda shima, ya taka rawar gani, a yunƙurin warware rikicin ƙasar, a lokacin da ya riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar AU.

A nasa ɓangare, nan gaba a yau ne, shugaban kasar Cote d´Ivoire Lauran Bagbo, zai gana da shugabanin rundunar tawaye, da ta gwamnati, domin masanyar ra´yoyi, a game da inda a ka kwana, a tantanawar kwace ɗamara, da sauran batutuwan da su ka shafi rikicin ƙasar.