1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Koffi Annan a Isra´ila

August 29, 2006
https://p.dw.com/p/BulC

Sakatare Jannar na Majlisar Dinkin Dunia Koffi Annan, na ci gaba da ziyara aiki a kasar Isra´ila.

Jim kadan bayan wannan ziyara saidai ya kai rangadi a sassanonin rundunar shiga tsakani ta Majalisar Ɗinkin Dunia dake kudancin Libanon.

Koffi ya gana da ministan tsaro Amir Peretz, sannan gobe idan Allah ya kai mu, zai tantana da Pramninista Ehud Olmert.

Babban burin da ya ke buƙatar cimma, shine ɗage takunkumin zirga zirga, ta ƙasa, ta ruwa da ta sararin samaniya, da Isra´ila, ta sarƙafawa Libanon.

A ganawar da yayi jiya da hukumomin Beyruth, Koffi Annan, ya yi kira ga ƙungiyar Hizbullahi, ta yi belin sojoji Isra´ila da ta kame.

Ya bayyana burin Majalisar Ɗinkin Dunia, na tabbatar da kwanciyar hankali a yanki gabas ta tsakiya baki ɗaya.

Annan ya ci gabada cewa

A nata ɓangare ministar harakokin wajen Isra´ila Tzipi Livni, ta tantana yau da hukumomin Danmerk.

A wani taron manema labarai da ta kira, ta sanar cewa Isra´ila ba za ta ɗage takunkumin zirga zirga da ta sakawa Libanon ba, sai lokacin da dakarun Majalisar Dinkin Dunia su ka ɗauki yaunin kulla da yanki.