1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia a Afrika

June 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuIX

islama.

Tawagar komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia na ci gaba da rangadi a wasu ƙasashen nahiyar Afrika.

Bayan Ethiopia da Sudan , a yau tawahar za ta Ghana da shugaban ƙasar Ghana, bugu da ƙari shugaban ƙungiyar taraya Afrika John Kuffor.

Jikadan Britania a Majalisar Ɗinkin Dunia, Emyr John Spade ya bayyana matukar gam,suwa da sakamakon da su ka cimma, tare da hukumomin Karthum a game da rikicin yankin Darfur.

Shugaba Omar Al Bashir a wani mataki na ba zata, ya amince ba tare da gitta sharaɗi ba,ya karɓi tawagar shiga tsakani a yankin Darfur, wadda zata ƙunshi dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia, da na ƙungiyar taraya Afrika.

Komitin Sulhu ya ƙudurci tura dakaru dubu 20 a yankin Darfur, wanda za su taimaka a kawo ƙarshen tashe-tashen hankullan da ke wakana, matakin da aka daɗe a na kai ruwa rana a kann sa.

Jikadan Britania ya yi kira ga yan tawayen Darfur suma ,su bada haɗin kai, a wannan saban babe da a ka shiga, ta fannin kawo ƙarshen rikicin yankin, wanda ya zuwa, ya hadasa mutuwar mutane fiye da dubu ɗari 2.