1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Mahmud Abbas a nahiyart turai

February 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuRF

Shugaban Palestinawa Mahmud Abbas yayi kira ga kasashen duniya da su janye matakan dakatar da taimako ga gwamnatin Palestinu. A lokacin da ya ke jawabi, bayan ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin jiya juma’a, ne, shugaba Abbas yace matakan kakabawa hukumomin Palestinu takunkumin tattalin arziki ba kann ka’idojin shari’a bane, kana ya yi kira ga wadanda abin ya shafa, da su hanzarta wajen dakatar da wannan mataki. A nata bangaren, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi murna da yarjejeniyar da aka cimma tsakannin kungiyoyin Fatah da ta Hamas mai zazzafan ra’ayin Islama, ta kafa gwamnatin hadin gwiwa, amma bata yi wani bayani akan matsin lamba daga kungiyar Tarrayyar Turai na tilasatawa duk wata gwamnatin hadin gwiwar da za’a kafa, akan amincewa da wanzuwar kasar Israila ba, amma ta sake jadadda kira ga gwamnatin Palestinu akan ta saki sojin nan dan Israila da take tsare da shi.