1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara ministan harakokin wajen Jamus a kasar Amurika

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2w

A ƙarshen ziyara aiki da ya kai a ƙasar Amurika, Ministan harakokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir, yayi kira ga gwamnatin Amurika, da ta shiga tantanawar ƙeƙe da ƙeƙe, da Iran, domin kawo ƙarshen rikicin makaman nuklea.

Saida, bayan ganawar da yayi, da sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, Steinmeir, ya gano cewar Amurika ba ta da wata aniya, ta amincewa da wannan tayi.

Ga alamamu, ministan ya ɗora alhakin ƙiƙƙi-ƙaƙar da a ke fuskanta ga Iran, ta la´akari, da gwajin da ta yi, shekaran jiya, na wassu sabin makkamai, masu lizami.

Wannan gwanji inji Steinmeir, wani mataki ne,na tsokanar faɗa, kazalika, ya na da mattukar tayar da hankali, idan a ka tuna, da kalamomin shugaban ƙasar Iran, Mahamud Ahmadi Nedjad, a game da burin sa, na shafe Isra´ila daga doran ƙasa.

Frank-Walter Steinmeir, yayi kira ga Amurika, da ta yi anfani, da tantanawar da ta ke, da hukumomin Iran, a game da rikicin Irak,domin soka batun matsalolin makamman nukela.