1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara ministan harakokin wajen Jamus a kasar Jordan

February 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7x

Ministan harakokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier, na ci gaba da ziyara aiki ,a yankin gabas ta tsakiya.

Bayan kasar Palestinu, da ya ziyarata da sahiyar yau, ministan ya sauka ,a kasar Jordan.

A Palestninu ya gana da shugaban hukumar Palestinawa, Mahamud Abbas, inda su ka tantana, a kan batutuwa daban daban, da su ka shafi harakokin diplomatia tsakanin Jamus da Palestinu.

Mussaman sun yi massanyar ra´ayoyi a game da harakokin siyasar kasar bayan nasara da kungiyar Hamas ta samu, a zaben yan majalisun dokoki na ranar 25 ga watan janairu da ta wuce.

Kazalika ministan harakokin wajen Jamus, ya kiri dukkan kasashen dunia, da su mayar da Hamas saniyar ware, har lokacin da, ta ci ka sharrudan da kasashen su ka gindaya mata.

A yanzu haka ministan harakokin ketare na Jamus na kasar Jordan.

A wani taronmanema labarai da ya jagoranta ya gayyaci kasashen dunia da su zama tsintsiya madaurin ki daya, domin fuskantar kalubalen Iran, na sarrafa makaman nuklea.