1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara N .Sarklozy a Afrika

July 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuGd

Shugaba Nikola Sarkozy na France, ya kai ziyara farko a nahiyar Afrika, a matsayin sa na shugaban ƙasa.

A matakin farko Sarkozy ya ziyarci Algeria, ta la´akari da tarihin da ya haɗa France da wannan ƙasa.

Ya gana da takwaran sa, AbdulAziz Buteflika, inda su ka tantana, a game da al´ammura daban-daban da su ka jiɓanci tattalin arziki, diplomatia, da shigi da ficin al´umma, tsakanin Afrika da France.

Tawagogin ƙasashen2, sun tantana, a game da saye da sayarawa ta fannin makamashi.

Bayan birnin Algers shugaba Sarkozy, ya ta shji zuwa Tunisia.

A cewar kakakin fadar Elysee, babban burin wannan rangadi, shine gudanar da masanyar ra´ayoyi a game da burin shugaban ƙasar France a kann batun mu´amila tsakanin dukkan ƙasashen da ke ɓangarori daban-daban na gaɓar teku.