1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Nikola Sarkozy a Afrika

July 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuFL

Shugaban ƙasar France Nikola Sarkozy, ya shiga kwana na 3, kuma na ƙarshe, a aikin sa yara ta farko a yankin Afrika kudancin Sahara.

Sarkozy ya farao wannan rangadi da ƙasar Lybia,sannan ya sauka jiya a birnin Dakar na ƙasar Senegal, inda ya tanttana da shugaba Abdullahi Wade, a game da hulɗoɗi tsakanin Senegal da France.

Kazalika, sun yi masanyar ra´ayoyi ,a game da wata sabuwar taswirar mu´amila, tsakanin Afrika da France, da shugaba Sarkozy ke buƙatar ƙirƙirowa.

Saidai a matakin ƙasar Senegal, jama´a da dama,ta nuna adawa da ziyara Sarkozy, wanda su kewa kallon maƙiyin Afrika.

A yanzu haka, shugaban France na ƙasar Gabon, inda ya ke ci gaba da ganawa da takwaran sa Omar Bango.