1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Nikola Sarkozy a Russia

October 9, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8v

Nan gaba a yau ne shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy, zai fara ziyara sa ta farko a ƙasar Russia.

A jajibirin wannan rangadi, hukumomin Mosko, sun hiddo sanarwa, inda su ka bayana buƙatar su, ta yin anfani da wannan dama, domin samun haske a game da matsayin France, akan harakokin siyasa da na na diplomatia da dama, na ƙasashen dunia.

Mosko ta ambata tantanawa da tawagar France, a game da rikicin gabas ta tsakiya, da taƙadamar nulear ƙasar Iran.

Idan dai za iya tunawa, a watan da ya wuce, an samu saɓanin ra´ayoyi, tsakanin shugaban ƙasar France, da minsitan harakokin wajen sa, Bernard Kouchner, a game da rikicin na Iran.

Russia da ke ɗaya daga ƙasashen da ke bada goyan baya ga hukumomin Teheran, na buƙatar samun cikkaken matsayin France, a dangane da wannan rikici.

Sannan, za su masanyar ra´ayoyi, a dangane da matsayin Kossovo , da kuma al´amarin da ke wakana a yankin Darfur na ƙasar Sudan.