Ziyara Paparoma a majami´ar Sagrada Familia
November 7, 2010Shugaban ɗariƙar Roman Katolika Benedikt na 16 ya jagoranci bikin buɗa majami´a Sagrada Familia a birnin Barcelona na ƙasar Spain.Yau shekaru kusan 130 aka fara ginin wannan majami´a amma har yanzu da sauran aiki. A na sa ran ƙara kwashe shekaru 15 kamin a kammala komai.
A cikin addu´o´in da ya yi, Paparoma ya roƙi Allah ya ƙara jawo hankalin mabiya addinin krista domin su ƙara himmantuwa wajen aiyukan ibada.
Sai dai jim kaɗan kamin tada sallar, sai da ´yan luwaɗin ƙasar Spain, su ka shirya wani gangami domin nuna adawa ga ziyarar Paparoma, tare da yi masa kalamomin ɓatanci.
Zanga-zangar na matsayin martani ga matakin Fadar Vatican na yin Allah wadai ga auratayya tsakanin´yan luwaɗi.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal