1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Paparoma Benedict a ƙasar Cyprus

June 4, 2010

Tattaunar butun samar da zaman lafiya tsakanin musulmi da krista shine makasudin ziyara ta Paparoma

https://p.dw.com/p/NiOJ
Paparoma Benedict XVIHoto: AP

 Paparoma Benedict  na 16 ya fara wata ziyara a yau  a tsibirin Cyprus,

 Benedict wanda yanzu haka ya yadda zango a birnin Paphos wanda ke kudanci ƙasar, zai kwashe kwanaki ukku ya na yin ziyara a ƙasar da galibi yan ɗariƙar Orthodoxe suke da rinjaye.

Wannan ziyara ta sa da ita ce ta farko da wani jagoran shugaban ɗariƙar roman katolika ke yi a tsibirin, na shan suka daga shugabanin ɗariƙar Orthodoxe.

Maƙasudin ziyara tasa dai shine wani kundin aiki da Paparoman zai miƙa ga wasu fada fada guda 12 ,wanda zasu duba wasu muhimman bututuwa na yankin gabas ta tskiya a taron da ake shirin na gaba a cikin watan Oktober a fadar Vatican da kuma butun tattaunawa tsakanin musulmi da Kirista domin samar da zaman lafiya

Mawallafi : ABdourahamane Hassane

Edita        : Yahouza sadissou Madobi