1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Robert Zoellick a kasar Sudan

November 10, 2005
https://p.dw.com/p/BvLl

Mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amurika Robert Zoellick na ci gaba da ziyara aiki a kasar Sudan.

A wata lacca da ya gabatar jiya, gaban dalliban jami´ar birnin Khartum, Zoellick ya bayana cewar idan ba a yi ba takatsantasan ba,ci gaban yakin yanki Darfur kan iya tabarbara da yarjejeniyar zaman lahia da ka cimma da yan tawayen kudancin Sudan; Idan kuwa hakan ta wakana, ba karamin koma baya ne ba, ga kasar baki daya da kan iya fadawa yanayin yaki gama gari.

Robert Zoellick yayi kira ga yan tsafin yan tawayen SLM da su rikida zuwa jamiyar siyasa, su ka rike mukamai daban daban da aka tanadar masu a madafin mulki.

A daya bangaren ya gayyaci yan tawayen Darfur da su bada hadin ka,i domin cimma yarjejeniar zaman lahia a taron sulhu da za a komawa ranar 22 ga wata da muke ciki a birnin Abuja na Tarayya Niogeria.

Nan gaba a yau ne, Robert Zoellick zai ziyarci yankin Darfur bayan ya gana jiya da shugaban Omar El Beshir.