1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Robert Zoellick a Sudan

Yahouza sadissouNovember 10, 2005

Mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amurika Robert Zoellick na ci gaba da ziyara aiki a kasar Sudan

https://p.dw.com/p/Bu4M

Mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amurika, Robert Zoellick na ci gaba da ziyara aiki da ya kai a kasar Sudan.

A wata ganawa da yi da matasa na jami´ar birnin Khartum Zoellick ya ja hankulan su a game da yaunin da ya rataya a kan su zuwa gaba na jagorancin kasa.

A dangane da rikicin da Sudan ke huskanta, ya bayanna cewa tabarbarewar al´ammura a Darfur, na da matukar hadari, ta fannin maida hannun agogo baya, ga yarjejeniyar zaman lahia da a ka cimma, tsakanin yan tawayen kudancin Sudan, da gwamnati, a watan janairu na wannan shekara, wanda a sakamakon sa, a ka kawo karshen shekaru 21 na yakin bassasa a yankin.

Robert Zoellick yayi kira ga tsofin yan tawayen kungiyar SLM ,ta mirganyi John Garang, da su rikadar da wannan kungiya zuwa jam´iya, ta yadda za su taka rawa gani a fagen siyasar Sudan, su kuma samu karamci daga kasashen dunia.

Ya kuma bukaci su ci gaba, da rike da rike mukamai daban daban, da aka yi masu tanadi, a yarjenejiyar da su rataba hannu tsakanin su da gwamnati.

Idan su ka rike wannan matsayi, ko shaka babu, inji sakataran na harakokin waje, Amurika zata ci gaba da basu tallafi da hadin kai.

A daya gefen ,yayi kira ga yan tawayen Darfur da su yi koyi da yan kudancin Sudan, su hada kai, domin cimma yarjejeniya da gwamnati, a tebrin shawarwari sulhu, da za a koma ranar 22 ga watan da mu ke ciki, a birnin Abuja na tarayya Nigeria.

A ranar jiya, Zoellick ya gana da shugaban kasa Omar El Beshir inda su ka yi masanyar ra´ayoyi ,a game da inda a ka kwana, a alkawuran da bangarori su ka dauka a yarjejeniyar sulhu, tsakanin Gwamnati da kungiyar SLM, da kuma yada a ke ciki a warware rikicin yankin Darfur.

A yau mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amurika, zai kai rangadin gani da iddo, a yankin Darfur.

Ranar talata da ta wuce ya yada zango a Kenya inda a nan ma su ka tantana akan matsalar tawaye a kasar Sudan.

Wannan ziyara, itace irin ta, ta 4 da Robert Zoellik ya kayo a shekara da mu ke ciki a kasar Sudan.

Ya sannar cewa babban burin da Amurika ke bukatar cimma, shine na tabbatar da zaman lahia mai dorewa a wannan kasa da ke fama da riginginmun tawaye.

Ta wannan fannin ne,ma Praminstan kasar Kanada Paul Martin ya sannar a jiya, cewa Kanada za ta tura wata tawaga ta musamman, a yankin Darfur, domin tantance hanyoyi da fannoni, daban daban na tallafin da Kanada ke iya kawowa domin warware takkadamar da ta ki ci at ki cenyewa a wanna yanki.

Wannan zata kai ziyara daga 11 zuwa 20 ga watan november.

Tawagar bisa jagorancin Ambassada Robert Fowler da Jannar mai ritaya Romeo dallaire, zata tantanawa da hukumomin kasar Sudan da shugabanin yan tawaye da kuma rundunar shiga tsakani, ta Kungiyar taraya Afrika, da tawagar Majalisar Dinkin Dunia.