1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Romano Prodi a nahiyar Turai

June 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuuG

Saban shugaban gwamnatin Italia ,Romano Prodi ya fara wani rangadi a nahiyar turai, wanda shine na farko, tun bayan da ya hau wannan muƙami.

Romano Prodi, ya fara wannan rangadi da birnin Viena, na ƙasar Austriya, inda ya gana da shugaban gwammnati Wolfgang Schüssel, wanda a halin yanzu ,ke rike da matsasayin shugaban ƙungiyar gamayya turai.

Romano Prodi, ya ƙudurci aniyar farfado da daftarin tsarin mulkin EU, bayan da al´ummomin ƙasashe France, da Holland su ka yi wasti, da shi a shekara da ta gabata.

Nan gaba a yau, shugaban gwamnatin na Italia ,zai gana da shuagaban ƙasar France Jaques Chirac.

Ba ada bayan batun kundin tsarinmulkin EU, magabatan na tanatana batun karɓar ƙasashen gabacin turai, kamar Roumania, Bulgaria, Serbia, da dai sauraran su , a cikin EU.

Romano Prodi, zai anfani da wannan dama, domin tabbatar wa takwarorin sa na EU, cewar Italia, a shire ta ke, fiye da shekarun baya, na yin aiki tuƙuru, domin ci gaban EU.

Idan ba a manta ba, Romano Prodi ya riƙe, matasyin shugaban komitin zartaswa, na wannan ƙungiya wace a halin yanzu, ta ƙunshi ƙasashe 25.