1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara shugabar gwamnatin Jamus a ƙasar Rasha

July 15, 2010

Angela Merkel ta tattauna butun hulɗa da kasuwanci da shugaba Dmtri Medevedev na ƙasar Rasha.

https://p.dw.com/p/OMls
Shugaban ƙasar Rasha Dmitry Medvedev, da Angela Merkel Shugabar' gwamnatin JamusHoto: AP

Shugaban ƙasar Rasha Dmtri Medvedev ya yi kira ga mayan kamfanonin na ƙasar Jamus da su saka jari a ƙasarsa, domin kawo canji na zamani ga al'amuran tattalin arziki na ƙasar.

Mista Medevedev da ke magana a gaban shugabar gwamnatin ƙasar Jamus Angela Merkel, wacce ta kai ziyara a ƙasar ta Rasha ,ya shaida cewa ƙasarsa na buƙatar goyon bayan ƙasar Jamus domin yin hoɓɓsa akan sha'anin tattalin arziki.

A dai wannan ziyara kamfanonin ƙasar Jamus da dama sun sa hannu tsakaninsu da gwamnatin ta Rasha akan yarjeniyoyi na kasuwanci.

Sanan Merkel ta yi fatan ganin Rasha ta gaggauta shigowa cikin ƙungiyar cinikayya ta duniya wato WTO kana kuma ta ci-gaba da cewa:"Za mu ci-gaba da tattaunawa a tsawon lokuta da dama tare, akan bututuwa masu muhimmanci dakuma tsauri".

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Ahmmad tijani lawal