1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara shugabar Swuizland a Afrika

July 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuGc

Ita ma Shugabar tarayya Swuizland, Micheline Calmy-Rey, ta fara rangadi a wasu ƙasashe 7 na nahiyar Afrika.

A matakin farko, ta yada zango a ƙasar Benin,inda ta bayyanawa shugaban ƙasa, Thomas Yayi Bony gamsuwa, a game da girkuwar demokraɗiya da kuma hoɓa sarmar hukumomin Porto Novo, babban-birnin ƙasar, ta fannin yaƙi da talauci.

Micheline Calmy-Rey, ta ce demokradiyar ƙasar Benin abun koyi ce, ga sauran ƙasashen Afrika, a game da haka ƙasar ta cencenci samu ƙarfin gwiwa daga Swuizland.

Tawagogin ƙasashen 2, sun rattaba hannu a kann yarjejniyoyi da deama, fannin kiwon lahia, yaƙi da jahilci da kuma inganta tsarin mulkin demokradiya.

Bayan Jamhuriya Benin, shugaabr tarayya Swuizlana za ta kai raagadi a ƙasashen Ghana, Senegal, Tchad, Jamhuriya Demokradiyar Kongo, Burundi da Rwanda.