1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Tony Blair a Afrika

May 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuKN

Praministan Britania Tony Blair, ya fara rangadin ban kwana a nahiyar Afrika.

Blair, da zai sauka daga karagar mulkin Britania, a wata mai kamawa, ya fara yada zango a ƙasar Lybia yau talata, kamin ya zarce zuwa Liberia, da kuma Afrika ta Kudu.

Kakakin Praministan ya ce Tony Blair, zai tantana da shugabanin wannan ƙasashe, a game da hanyoyin ƙarfafa mu´amila, tsakanin su da Britania , kazalika za su masanyar ra´ayoyi an a game da halin da ake ciki a nahiyar Afrika, ta fannin yaƙi da talauci da tashe-tashen hankullan da ke gudana a wasu ƙasashen nahiyar.

Wannan ziyara na wakanan a yayin da ya rage mako ɗaya a shirya taron shugabanin ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki na dunia, a nan ƙasar Jamus.

A tsawan shekaru 10 da yayi a kan karagar mulkin Britania, Tony Blair ya bayyana zama kakakin Afrika, a yunƙurin ta, na magance matsalolin fatara da talauci.