1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ziyara Tony Blair a Australia

March 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv46

Praministan Britania Tony Blair, ya fara ziyara aiki a ƙasar Australiya, matakin farko, na rangadin da zai kai shi a Indonesia, da Nouvelles Zelandes, ko kuma new Zelande.

Tony Blair, ya sauka a birnin Melbourne, da ke kudu maso gabacin ƙaysar inda zai halarci ƙarshen gasar wassanin ƙasashen Commonwealth.

Bayan kammalla wassanin, zai gana, da takwaran sa, John Haward na Australiya, sannan ya gabatar da jawabi a majalisar dokokin ƙasar, a kan mahiman batutuwa, da su ka haɗa da, yaƙi da ta´adanci ,da kuma kariyar mahhali.