1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Ahmedinejad a Algiers

August 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuEY

Shugaban kasar Iraan Mahmooud Ahmedinejaad,ya fara rangadin aiki na yini biyu a birnin Algiers,ziyarar dake da nufin inganrta dangantaka tsaskanin kasarsa da Algeria,adaidai lokacin da Iran ke cigaba da fuskantar matsin lamban kasashen duniya,dangane da sghirin nuclearnta.Kafofinyada labarun Algerian dai sun soki wannan ziyara ta Ahmedinejad, wadda ke zama irinsa ta farko da shugaban na Iran yakai zuwa wannan kasa dake yankin arewacin Afrika.

Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflike yayiwa takwaran nasa kyakkyawar maraba, a filin saukan jiragen sama,ayayinda akesaran zasuyi wata ganawa a wani lokaci yau da yammaci.

Ayayinda yake wannan kasa,Shugaban na kasar Iran zai kuma gana da yan kasuwa,kafin ya kammala ziyarar tasa a gobe talata.