1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar aiki ta farko da ministan tsaron Jamus Jung ya kai Washington

Mohammad Nasiru AwalDecember 20, 2005

Ministan ya ce tattaunawar da suka yi da jami´an gwamnatin Amirka ta yi armashi.

https://p.dw.com/p/Bu3G
Ministan tsaron Jamus F.-J. Jung
Ministan tsaron Jamus F.-J. JungHoto: AP

Kai kawon da yayi tsakanin ma´aikatar tsaro ta Pentagon da ta harkokin waje da kuma ganarwar da yayi a fadar White House da mai bawa shugaba Bush shawara akan harkokin tsaro Stephen Hadley, ya sa sabon ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung ba samu isasshen lokacin zantawa da ´yan jaridu ba. To amma ya bayyana tattauwar da yayi da cewa ta yi armashi, musamman dangane da manufar wannan ziyara, wato samar da yanayi na kara yarda da juna. Ziyararsa a ma´aikatar tsaron dai ta dauki lokaci fiye da yadda aka tsara, amma a karshe ministan tsaron na Jamus ya ce tattaunawar da yayin ta haifar da kyakkyawar hulda tsakaninsa da Rumsfeld.

“Ina tsammanin daidai ne kuma yana da muhimmanci a kawad da bambamce-bambamcen siyasa daga manufofin ketare da na tsaro. To sai dai ba sabon abu ba ne idan na nuna cewar dole a dora dangantakarmu da Amirka akan wani kyakyawan harsashi.”

Tun gabanin ya kai wannan ziyara, Jung da abokan tattaunawar sa na Amirka suka dace kan cewar ba su tabo batutuwan nan da ake cecekuce a kai ba. Saboda haka ministan tsaron na Jamus bai tabo maganar wani Bajamushe dan asalin kasar Lebanon Khaled El-Masri da hukumomin leken asirin Amirka suka yi garkuwa da shi har tsawon watanni 5 da kuma sufuran jiragen saman hukumar CIA cikin sirri a Jamus ba. Jung na mai ra´ayin cewa ba´a bukatar wani karin bayani bayan tattaunawar da aka yi akan wannan batu tsakanin sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice da SGJ Angela Merkel a farkon wannan wata.

A game da wani taimako da jamus zata bayar a kokarin da Amirka ke yi na samar da zaman lafiya da tsaro a Iraqi kuwa dan siyasar na jam´iyar CDU ya dage kan cewar Jamus ba zata tura dakrunta Iraqi ba. Sannan ya kara da cewa.

“Ina mai farin ciki cewar gwamnatin Amirka ta amince kuma take girmama matsayin Jamus a dangane da batun na kasar Iraqi, kana kuma ta yi maraba da taimakon horas da jami´an tsaron Iraqi da muke yi a cikin kasar hadaddiyar daular Larabawa.”

An kuma yi musayar ra´ayoyi akan halin da ake ciki a Afghanistan to amma ba´a tabo bukatar nan da Amirka ta gabatar ta hade aikin rundunar ISAF da aikin yaki da ta´addanci da Amirka ke yi a wannan kasa ba. Maimakon haka Jung ya goyi da bayan shawarar da tsohon SGJ Gerhard Schröder ya bayar dangane da yiwa kungiyar tsaro ta NATO sahihan sauye sauye a fannonin dubarun yaki da na siyasa.

A dangane da Iran kuwa ra´ayin Jamus da Amirka ya zo daya cewar dole ne a dauki matakan da suka dace akan wannan kasa bayan sabuwar kataborar da shugaba Mahmud Ahmedi Nijad yayi na saka ayar tambaya game da wanzuwar kasar Isra´ila da kuma karyata kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa. Dole ne kuma a ci-gaba da shawarwari tsakanin tarayyar Turai da Iran akan shirinta na nukiliya, domin kera makaman nukiliya a Iran ba abin karbuwa ba ne ga gwamnatocin Washington da Berlin.