1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR AIKIN SCHROEDER A NAHIYAR AFRICA

JAMILU SANIJanuary 19, 2004
https://p.dw.com/p/BvmU
Yanzu haka dai shugbana gwamnatin Jamus Gehard Schroeder ya fara gudanar da ziyarar aikinsa a nahiyar Africa a yau litinin,inda ya fara ziyartar kasar Habasha don tabatar da ganin an samo hanyoyin kawo karshen rikicin kann iyaka dake tsakanin kasahen Habasha da Eritrea. Bayan ganawarsa da shugaban gwamnatin Jamus Gehard Schroeder,Priministan kasar Habasha Meles Zenawi ya bukaci Schroeder da yayi bakin kokarinsa wajen ganin an samo hanyoyin warware rikicin kann iyaka dake tsakanin kasahen Habasha da Eritrea,da aka shafe kusan shekaru hudu ana fama da shi,wanda kuma ya jawo salwantar rayukan alumomin kasahen biyu na kahon Africa.

Da yake jawabi ga manema labaru,Pm na kasar Habasha Zenawi,ya baiyana cewa Schroeder ya tabatar masa da cewa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya taimaka an sami masalaha ta zaman lafiya tsakanin Habasha da Eritrea. Shugaban gwamnatin dai ta Jamus ya baiyana cewa baban fatan Jamus shine a kai samar da masalaha za sulhu tsakanin kasahen biyu na kahon Africa ba tare da an cigaba da baiwa Hamata Isska ba. Bugu da kari Pm na kasar Habash Meles Zenawi,ya baiyana cewa aa yayin tattaunawar da Schroeder,sun jadada bukatar dake akwai ta ganin aan sami tabatacen zaman lafiya a yakin kasahen Kahon Africa.

Ziyarar aikin dai ta Schroder a nahiyar Africa ita ce irin ta farko tun lokacin da ya dare kann karagar mulki a shekara ta 1998,kuma tun a jiya lahadi ya fara gudanar da wanan ziyarar aiki da zata kashi kasahen Kenya,Africa ta kudu da Ghana.

Da yake jawabi ga jami'an diplomaciya na kasahen Africa a hekwatar kungiyar gamaiyar Africa dake birnin Adis Ababa,Schroder yayi alkawarin cewa gwamnatin jamus zata bada taimako na kudade wajen kafa cibiyar horas da aiyuka na kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa ta Kofi Anan a birnin Accara na kasar Ghana. Shugaban gwamnatin dai ta Jamus ya kara da cewa gwamnati a birnin Berlin zata baiwa kungiyar gamaiyar Africa taimako na Euros Miliyan 650,don ta sami sukunin bunkasa aiyukanta na kiyaye zaman lafiya a nahiyar Africa. Haka zalika gwamnatin Jamus ta yi alkawarin bada taimako ga kungiyar habaka tattalin arzikin kasahen Africa ta (NEPAD) a takaici da aka kafa da nufin bunkasa harkokin zuba jari da kuma samar da cigaban tattalin arzikin kasahen nahiyar Africa baki daya.

Bugu da kari gwamnati a birnin Berlin ta yi alkawarin bada horo ga soji da kuma sauran jami'an gwamnati a dukanin kasahen yammacin Africa.

Tun shekara ta 1998 rikicin kann iyaka ya barke taskanin kasahen Habasha da Eritrea,inda wanan hali yayi sanadiyar mutuwar alumomin kasahen biyu na kahon Africa 80,000. Schroeder da Zenawi sun rataba hanun kann yarjejeniyar harkokin zuba jari a tsakanin kasahen biyu. Yau ne kuma ake sa ran Schroeder zai kai ziyarar aiki a kasar Kenya,kafin kuma daga bisani ya wuce zuwa kasahen Africa ta kudu da Ghana.