1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIyarar Angela Markel a birnin Paris

YAHAYA AHMEDJuly 19, 2005

Shugaban jam’iyyar CDU, Angela Merkel, ta kai ziyara a birnin Paris, inda ta gana da shugaba Jacques Chirac na Faransa, don tattauna batun matsayin huldodi tsakanin Jamus da Faransa, da kuma yadda al’maura za su kasance idan ta lashe zaben da za a gudanar a nan Jamus a cikin watan Satumba mai zuwa, ta zamo shugabar gwamnatin tarayyar Jamus.

https://p.dw.com/p/Bvan
Angela Merkel da shugaba Chirac na Faransa, yayin ziyarar da ta kai masa a fadar Elysee a birnin Paris.
Angela Merkel da shugaba Chirac na Faransa, yayin ziyarar da ta kai masa a fadar Elysee a birnin Paris.Hoto: dpa

A halin yanzu jam’iyyun adawa a majalisar dokokin Jamus, wato CDU da CSU, na dokin isowar watan Satumba. Saboda a cikin wannan watan ne bisa dukkan alamu za a gudanad da zaßen majalisun tarayya, inda kuma suke fatar samun gagarumin nasara, don su iya kafa gwamnati. Idan ko fatarsu ta tabbata, to a karo na farko a tarihin Jamus, za a sami mace ke nan a shugabancin gwamnatin tarayya. Wadda kuwa ke fafutukar hawar wannan mukamin, ita ce Angela Merkel, shugaban jam’iyyar adawa ta CDU, wadda kuma ita ce za ta tsaya takara a zaßen, don ta kalubalanci shugaban gwmantin tarayya Gerhard Schröder.

A halin yanzu dai, shugaba Schröder da shugaba Jacques Chirac na Faransa na da kyakyawar hulda tsakaninsu. Game da hakan ne ma jam’iyyun adawa ke zargin Schrödern da yin watsi da sauran kasashen kungiyar Hadin Turai, don faranta wa Faransa rai. A cikin manufofin yakin neman zaßensu, jam’iyyun sun tanadi sake siffanta tsarin huldodi tsakanin Jamus da Faransa, idan suka ci nasara. Sun ce hakan zai kara daidaita huldodin Jamus da sauran kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai.

Babu shakka, Jacques Chirac da shugaba Schröder sun taka rawar gani, wajen tsara shirye-shirye da dama na inganta kafofin Kungiyar Hadin Kan Turai. Amma a halin yanzu, jama’a na dari-dari da amincewa da jawabansu. Da farko dai, duk kasashen biyu, sun sha saßa wa ka’idojin Kungiyar Hadin Kan Turan, da zarce haddin kashi 3 cikin dari na gißin kasafin kudinsu, ka’idar da kungiyar ta ajiye don kare darajar kudin Euro. Bugu da kari kuma, tun kin amincewa da al’umman Faransan suka yi da kundin tsarin mulkin Kungiyar EUn, a zaßen raba gardamar da aka gudanar a cikin watan Mayu ne, kwarjinin shugaba Chirac ya fara dusashewa a kasar.

Wannan sabon hali da aka shiga ciki dai, zai iya janyo wani gagarumin sauyi a yadda ababa za su dinga wakana a harkokin Kungiyar Hadin Kan Turai, inji Martin Koopmann, wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Jamus a birnin Berlin:-

„Mai yiwuwa, saboda dusashewar kwarjinin Faransa a Kungiyar Hadin Kan Turai, Jamus ta zamo jagorar kungiyar. Amma hakan zai wakana ne idan aka sami sauyi a gwamnatin ta Jamus, musamman ma dai idan Angela Merkel ta zamo shugaban gwamnati.“

Manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa, idan jam’iyyun adawa na CDU da CSU suka ci nasara a zaßen watan Satumba, har kuma suka fara jan ragamar mulki, to da alamun za a sami ßarkewar rikici tsakanin biranen Berlin da Paris. Da farko dai, a siyasar harkokin waje, Faransa da Jamus a halin yanzu, na cikin masu goyon bayan dage takunkumin sayad da makamai da Kungiyar EU ta sanya wa kasar Sin. Ita ko Angela Merkel, ko kadan ba ta son ganin an soke wannan takunkumin.

Inda kasashen biyu za su sami rashin jituwa kuma, idan Angela Merkel ta zamo shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, shi ne kan batun kare darajar kudin Euro. Jam’iyyun adawan na Jamus dai, na nanata cewa, idan suka hau karagar mulki, za su yi duk iyakacin kokarinsu wajen ganin cewa, an kiyaye ka’idar nan ta takaita gißin kasafin kudin ko wace kasa mai amfani da Euro a kashi uku cikin dari na kudaden shigarta a shekara. Shi ko shugaba Chirac, kokarin daga wannan haddin zuwa sama yake yi.

Ko me ake ciki dai, idan aka sami sauyin gwamnati a nan Jamus a cikin watan Satumba, huldodi tsakanin Berlin da Paris ba za su iya kaucewa daga hauhawar tsamari ba, sai kuma an yi wata sabuwar gwamnatin a Faransa. Wakanar hakan kuwa, za ta dogara ne kan sakamakon zaßen shugaban kasar da za a gudanar a cikin shekara ta 2007.

A halin yanzu dai, ana hasashen cewa, ministan harkokin cikin gidan Faransan, Nicolas Sarkozy, shi ne ke nuna alamar gadan mukamin shugaba Chirac. Shi ko Sarkozyn ba bako yake ga Angela Merkel ba. Tun da dadewa jam’iyyunsu na da hulda da juna. A ziyarar da ta kai a yau a birnin Paris ma, ganawa da shi Sakozyn na cikin ajandarta.