1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Angela Merkel a Italiya

December 20, 2005

Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, ta kai ziyararta ta farko a kasar Italiya tun hawarta a karagar mulki, inda ta gana da Firamiyan Italiya Silvio Berlusconi a birnin Rom.

https://p.dw.com/p/Bu3F
Merkel da Berlusconi
Merkel da BerlusconiHoto: AP

Ziyarar da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel ta kai a birnin Rom jiya, ta wakana ne cikin wani yanayi na sassaucin tsamari, inda murmushin mai karbar bakwancinta, Firamiyan Italiya Silvio Berlusconi ike bayyana hakan a zahiri. Babu shakka, shi dai Firamiyan na Italiya, ya gamsu da sauyin mulki da aka yi a birnin Berlin. A cikin wata fira da maneman labarai, ya bayyana cewa, a duk lokacin da ake ta gwagwarmayar kafa sabuwar gwamnati a Jamus, fatarsa ce Merkel ta sami nasara.

Wannan bayanin dai ba abin mamaki ba ne. Saboda, da can dai Shugaba Schröder na Jamus da Firamiyan na Itliya Silvio Berlusconi, ba sa jituwa sosai, a kan batutuwa da dama. A lal misali, a kan batun afka wa Iraqi da yaki, da Italiyan ta goyi bayansa, yayin da Jamus kuma ta nuna matukar adawa ga shirin. Hakan kuwa ya janyo wata hauhawar tsamari a dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A halin yanzu dai, Firamiya Berlusconi, ya kyautata zaton cewa, kasarsa da Jamus, za su mai da wannan batun baya, su dukufa kan inganta huldodi tsakaninsu.

Da take mai da martani, shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ba ta ambaci batun Iraqi ba. Amma ta goyi bayan shirin inganta huldodi tsakanin Berlin da Rom. Game da ma’ammala tsakaninta da Firamiya Berlusconi, Angela Merkel cewa ta yi:-

„Mun dai saba da juna a taruka daban-daban na jam’iyyun `yan mazan jiya na nahiyar Turai da muke halarta. Muna da ra’ayi daya. Kuma manufofin siyasarmu sun zo daidai, inda muke karfafa inganta halin rayuwar al’umma da kuma bunkasa harkokin tattalin arziki.“

Shugaban ta Jamus ta kuma bayyana cewa, bangarorin da kasashen biyu za su yi aikin hadin gwiwa a kansu, sun hada ne da shirin nan na yakan ta’addanci da kuma fafutukar samar da wata manufa ta bai daya ta kasashen nahiyar Turai, wajen tinkarar matsalar nan ta bakin haure. Game da makomar Kungiyar Hadin Kan Turai kuma, Merkel ta bayyana cewa, Jamus da Italiya na bin ra’ayi daya. Kamar yadda ta bayyanar:-

Mun san cewa a halin yanzu nahiyar Turai na huskantar wani gagarumin kalubale. Sabili da haka ne kuwa, ya kamata kasashe kamar Italiya da Jamus su karfafa matsayinsu, na kasancewa masu jagorancin fannin tattalin arzikin kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai. Kamata ya yi mu kasance kan gaba a fannin bincike da fasaha, don mu jagoranci Turai huskantar kalubalen da ke zuwa mata daga Asiya da sauran yankuna, ta yadda ba za a mai da ita a baya a harkokin ci gaban masana’antu a duniya ba.“

Firamiya Berlusconi dai, ya yabi Angela Merkel ne, game da irin namijin kokarin da ta yi, wajen cim ma daidaito a kan batun kasafin kudin Kungiyar Hadin Kan Turan nan da aka yi ta korafi a kansa.

A karshe dai, ya kyautata zaton cewa, shugaban ta Jamus ma, za ta dinga zuwa hutunta na bazara a Italiya kamar yadda tsohon shugaba gerhard Schröder ke yi.