1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Annan a sierra Leone

Zainab A MohammedJuly 3, 2006
https://p.dw.com/p/BtzR
Sakatare General na Mdd,Kofi Annan
Sakatare General na Mdd,Kofi AnnanHoto: AP

A yau ne sakatare General na Mdd Kofi Annan ya isa birnin Freetown din kasar Saleon,a wani rangadin aikin hukumomin majalisar dake wannan kasa ta yammacin Afrika,wadda ke farfadowa bayan kawo karshen yakin basasan shekaru 10 a shekarata 2001.

Kofi Annan wanda ya sauka a filin jiragen sama na kasa da kasa dake Lungi,ya samu kyakkyawar maraba daga ministan harkokin kasuwanci Kadi Sesay.

A wannan rangadin aiki nasa a wannan kasa da yaki ya dagargaza,jagoran MDD zai kai ziyara kotun majalisar dake sauraran shariar masu manyan laifukan yaki,ciki harda tsohon shugaban Liberia Charles Taylor.

Duk dacewa an kawo karshen yakin Saleon din a shekarata 2001,kasar na cigaba da kasancewa cikin mawuyacin hali na rayuwa saboda kanginrtalauci.

Mr Annan wanda ya isa Salaeon din a daren jiya,bayan kamala taron yini biyu na shugabanin Afrika a birnin Banjul din kasar Gambia,ana saran yau din zai gana da shugaba Ahmed Tejan Kabbah.

A karshen shekarar data gabata nedai ayarin kiyaye zaman lafiya na dakarun mdd da yawansu yakai dubu 17,suka fice daga wannan kasa,bayan kamala zaben kasar ,tare da tabbatar da zaman lafiya a wannan kasa bayan yake yaken shzekaru 10.

To sai dai manazarta na ganin cewa,ayyukan da mdd ta gudanar a wannan kasa zai iya tarwatsewa ,kasancewar saleon din daya daga cikin kasashe wadanda talauci yayi musu kanta.Kasar wadda ke yankin yammacin Afrika dai na fama da rashin wutan lantarki ,da rashin ruwan sha mai tsabta.

Bisa ga wannan ziyara ta Kofi Annan,da wannan hali da kasar ke ciki ne ,jaridun kasar sukayi ta rubuta sharhuna dake kira gareshi daya agazawa mummunan muhalli da kasar ke fama dashi,wanda ya sanya ta zame kasa da akafi samun mace mace masu yawa.

To sai dai bayan gazawan Mr Annan wajen tursasawa Sudan amincewa da dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a lardin Darfur,ya fadawa taron manema labaru a Banjul cewa,mdd zatayi aiki kafada da kafada da darun Au dake Darfur din,domin karfafa ayyukansu fiye da yadda suke a yanzu.

A yanzu haka dai sabado karancin kayan sufuri dana aiki,dakarun Afrika dake Darfur din sun gazashawo kan matsalolin rayuwa da alummar yankin ke cigaba da kasancewa ciki,inda kisan gilla da azabtar da fyade ya tilasta mutane million 2 da dubu dari 5 sun kaurace daga matsugunnensu,domin neman mafaka.

Mr Annan yace babu yadda zaa tura dakarun MDD ba tare da amincewar shugaba Omar Hassan Al.Bashir na sudan ba,sai dai yace zaa gudanar da wani taro a Brussels din kasar Belgium a ranar 18 ga wannan wata,inda zaa nemin agajin kayayyakin aiki wa sojojin Afrika dake Darfur,ayayinda a karshen wannan watan ne akesaran shugaban na Sudan zai gabatar tsarin shiri na watanni 6 masu gabatowa.