1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Bush a Indonesiya

YAHAYA AHMEDNovember 20, 2006

Shugaban Amirka, George W. Bush, ya isa a ƙasar Indonesiya, inda yake ziyarar sa’o’i 6 a ƙasar da ta fi yawan musulmi a duniya. Dubban mutane ne dai suka yi ta zanga-zangar nuna adawa ga ziyarar shugaban. Sabili da haka ne dai aka girke jami’an tsaro da shirin ko ta kwana don kwantad da duk wata tarzomar da za a taso.

https://p.dw.com/p/BtxP
Masu zanga-zanga game da ziyarar shugaba Bush a Indonesiya.
Masu zanga-zanga game da ziyarar shugaba Bush a Indonesiya.Hoto: AP

Mahukuntan ƙasar Indonesiya sun ɗau tsaurararn matakan tsaro da ba a taɓa gani ba a ƙasar, game da ziyarar da shugaban Amirka, George W. Bush, ya kai a birnin Jakarta. Duk duniya dai ta sa ido ne kan kan wannan ziyarar, saboda muhimmancin ƙasar Indonesiyan tamkar ƙasar da ta fi yawan musulimi a doron ƙasa. Shakka babu, jama’an ƙasar da dama ne suka shiga zanga-zangar nuna adawa ga ziyarar shugaban na Amirka, kama daga ƙungiyoyin musulmi masu tsautsaurar ra’ayi, da mabiya addinan gargajiya na ƙasar har ya zuwa ƙungiyoyin ɗalibai masu bin ra’ayin gurguzu, dukkansu sun fito a duk faɗin ƙasar suna Allah wadai ga shugaba Bush da kuma manufofinsa a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Ziyarar ta shugaba Bush a Indonesiyan, wadda ta awa shida ce kawai, ta fara ne yayin da ya sauka a filin jirgin saman soji na Halim kusa da birnin Jakarta. Manyan jami’an gwamnati da kuma jakadan Amirka a Indonesiyan ne suka tarbe shi. Ba da daɗewa ba ne kuma ya ta shi daga nan cikin jirgin sama mai saukar ungulu zuwa garin Bogor, mai nisan kimanin kilomita 50 a wajen birnin Jakartan, inda ya gana da shugaban ƙasar Indonesiyan Susilo Bambang Yudhoyono.

Duk da tsauraran matakan tsaron da aka ɗauka, rahotanni sun ce wasu masu zanga-zanga kamar su dubu, sun keta ƙawayan da jami’an tsaro suka yi wa garin na Bogor, har suka nufi cibiyar sadaswa, inda aka girke maneman labarai na ƙasa da ƙasa. Da kyar ne dai ƙarin ’yan sandan da aka turo suka iya shawo kan tarzomar. A sauran yankunan birnin, ɗimbin yawan jama’a sun ci gaba da zanga-zangarsu ta nuna adawa ga shhugaba Bush. Wasu daga cikinsu na cira kawalaye ɗauke da rubutun „Ya kamata a kashe Bush“.

Ita dai Indonesiyan muhimmiyar abokiyar hulɗar Amirka ce a yankin Kudu Maso gabashin Asiya, musamman a huskan yaƙi da ta’addanci. Kuma tana bukatar janyo masu zuba jarin Amirka zuwa ƙasar. Amma mafi yawan al’umman ƙasar, mai yawan jama’a kimanin miliyan ɗari 2 da 20, na matuƙar adawa ne da manufofin shugaba Bush ɗin, musamman a yankin Gabas Ta Tsakiya. Jama’a da dama da maneman labarai suka yi fira da su sun bayyana ɓacin ransu ne ga ɗaukin soji da gwamnatin Amirkan ke yi a Iraqi da Afghanistan, abin da suke gani kuma kamar farmakin gwamnatin Amirkan ne kan musulmi gaba ɗaya.

Duk da amincewa kan batutuwa da dama da Amirkan da Indonesiya ke yi, mahukuntan birnin Jakartan dai sun sha yin suka kan manufofin Washington a waɗannan ƙasashen, da kuma irin munafuncin da take yi a rikicin Isra’ila da Falasɗinu, inda a zahiri take nuna fiffiko ga ƙasar bani Yahudun Isra’ilan.

Ban da dai batun rikicin Gabas Ta Tsakiyan, shugabannin biyu sun kuma takalo batutuwan da suka shafi ilimi, da yaƙi da talauci, da matakan shawo kan murar tsuntsaye da yaƙi da ta’addanci.

Wannan ziysarar dai ita ce ta biyu da Bush ya taɓa kaiwa a Indonesiyan, a matsayinsa na shugaban Amirka.