1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR BUSH IRAQ

ABUBAKAR D. MANINovember 28, 2003
https://p.dw.com/p/BvnM
An bayyana kai ziyarar ba zata, da shugaban Amurka George W. Bush, yayi,zuwa kasar Iraqi, da cewar wata dubara ce, ta siyasar neman juya matsayin durkushewar da gwamnatin Amurka, karkashin shugabancin Bush din,ke cikin yi,da kuma faduwar kimar ta, a idanun Amurkawa. Watau dai wani salo ne, na neman kyautata matsayi da neman samun goyon baya. Masu nazarin harkokin yau da kullum dai, sunce,siyace tsagoranta kurum,kai wannan ziyarar, a ranar hutu ta biyu mafi darajja ga Amurkawa, baya ga hutun Kirsimati,wadda maimakon Bush din ya kasance tare da iyalin sa, kamar yadda dabi'ar Amurkawan take a wannan ranar, saiya zabi, ya kaiwa sojojin dake fagen fama, a Iraqi, ziyara,a inda ya samu jinjinawar wasu sojoji kimanin 600 din da suka taru, a tashar jiragen saman Baghadaza babban birnin kasar Iraqin,domin tarbar sa da kasancewa tare da shi, wajen liyafar cin abinci.
Wani farfesa na jami'ar San Francisco, ta Amurka, a fannin ilmin fannin siyasa,da nazari akan al'amurran yankin gabas ta tsakiya,Stephen Zunes,yace wannan ziyarar na iya kasancewa wani karin karfin gwuiwa ne ga sojojin dake cikin fama a kasar Iraqi, wadanda suke matukar bukatar a nuna masu cewar,Amurka tare da shugaban Amurkar na tare dasu. Shima Judith Kipper, masani akan lamurran yankin gabas ta tsakiya,na cibiyar huldar kasashe,cewa yayi,yana ganin sojojin Amurka dake kasar Iraqi kam, gwiwar su ta kare,kuma suna cikin matsala gaya, saboda wannan, lalle, ziyarar kwamanda rundunonin sojojin Amurkar, watau Bush, zuwa garesu, na kimanin awoyi 2n, zata dan basu wani dan kwarin gwuiwar da suke bukatarsa,koda yake dai, zuwan shugabanni, wurin sojojinsu a fagen daga ba sabon abu bane. Wannan kuwa yayi daidai da batun da daya daga cikin Amurkawan dake Iraqin,yayi, a inda James Echols dan shekaru 22 da haihuwa dan Luverne, Alabama,ya bayyana cewar, ya samu kwarin gwuiwa kwai,a bisa ganin yadda Bush ya kwaso hanya, ya kuma baro iyalansa, ya kawo masu wannan ziyarar. A cikin jawabin da Bush yayi gaban sojojin Amurkar, a Baghadazan, a Iraqin, ya ce yana cikin farin cikin gayyatarsa liyafar cin abinci, a lokacin da yake neman inda zai samu irin wannan liyafar, a cikin annashuwa da jin dadi.
Duk da kasancewar sojojin Amurkar a Iraqi sunyi ta jinjinawa Bush din, amma masu lura da al'amurran yau da kullum, din, na ganin cewar, a can gida inda ya koma, bayan kammala wannan ziyarar, tana kasa tana dabo daine, har yanzu, a yayin da mamayen da Amurka ke cikin yi akan kasar Iraqi, keta samu rashin goyon bayan mutanen kasar Amurkar, tun daga kashi 80 a cikin 100, goyon bayan keta, kara faduwa daga farkon watan Mayu, yakai kashi 42 a cikin 100,kamar yadda ra'ayin jama'a ya nuna, a cikin wani binciken da ya bayyana a ranar 19 ga wannan watan da muke ciki, a bisa yadda kasar Amurkar take ta tafka asarar sojojin nata a yakin sunkurun dake gudana a kasar Iraqin. A halin da ake ciki dai, kashi 55 a cikin 100 na Amurkawa, suke kin yanayin da Amurka ta fada a cikin a Iarqi,a halin da ake ciki yanzu din. Saboda haka, ko wannan ziyarar da wuya ta farfado da wani goyon bayan azo a gani, akan halin rashin goyon bayan da gwamnatin Bush ke fama dashi, a cikin gida Amurka, kamar dai yadda ziyarar da shugaban Amurka Lyndon Johnson, yakai a Vietnam, a inda aka nuna hotunashi,yana gaisawa hannu da hannu da sojojin dake fagen daga a can, bata taimakeshi ba, akan matsayin siyasar sa, a wannan kasa ta Amurkar ba. Masu lura da harkokin yau da kullum, dai, na ganin cewar, wannan ziyarar,ba zata fidda gwamnatin Amurka, karkashin jagorancin George W. Bush din, daga faduwa ba. Domin manufar gwamnatin akan kasashen ketare bata samun goyon bayan cikin gida, dada balle a waje.