1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Condoleezza Rice a gabas ta tsakiya

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buhf

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice na ziyarar mako guda a gabas ta tsakiya domin nazarin cigaban da aka samu na wanzuwar zaman lafiya a yankin. Ta fara yada da zango a saudi Arabia domin tattaunawa da sarki Abdullah inda daga nan zata nufi Masar da Israila da kuma yankin Palasɗinawa. Ziyarar, ita ce ta farko tun bayan da aka kawo ƙarshen yaƙin da ya gudana a Lebanon tsakanin Israila da Hizbullah. Wasu manazarta sun soki lamirin shugaba Bush da cewa bai maida hankali ba sosai wajen sulhunta rikicin Israila da Palasdinawa inda suke baiyana shakku cewa ziyarar ta Rice ba zata yi wani tasiri ba.