1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Condoleezza Rice a Nahiyar Asia

October 18, 2006

Amurka ta yi barazanar daukar matakan soji a kan koriya ta arewa idan ta kaiwa Japan farmaki

https://p.dw.com/p/Btxi
Condoleezza Rice da Ministan harkokin wajen Japan Taro Aso
Condoleezza Rice da Ministan harkokin wajen Japan Taro AsoHoto: AP

Bayan ganawar ta da ministan harkokin wajen Japan Taro Aso, Condoleezza Rice ta ce ko kadan Amurka ba zata zura ido ta kyale ba Koriya ta arewa ta yiwa makwabtan ta shiga hanci da kudndune ko kuma nuna musu fin karfi ba. Ta ce idan kuwa ta sake ta yin hakan to ba shakka dandana kudar ta domin kuwa Amurka zata maida martani da dukkan karfin ta na soji.

Matsayin Amurka shi ne ta tabbatar da cewa daukacin jamaá har ma da yan kasar Koriya ta arewa su sani cewa Amurka zata aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan ta bisa yarjejeniyar cudanni-in cude ka da suka kulla na bada kariya ga kasar Japan ta fannin tsaro. A halin da ake ciki Amurka na da sojoji kimanin 40,000 dake jibge a kasar Japan bisa yarjejeniyar tsaro da suka cimma tun bayan da aka ci kasar Japan da yaki a lokacin yakin duniya na biyu.

Condoleezza Rice tace manufar ziyarar ta a kasashe hudu na yankin Asia shine domin neman goyon bayan su a dangane da aiwatar da takunkumin da Majalisar dinkin duniya ta sanyawa Koriya ta arewa bayan gwajin da Pyongyang ta yi na makaman nukiliya a makon da ya gabata. Ziyarar ta Condoleezza Rice ta zo ne a daidai lokacin da wasu bayanan sirri ke nuni da cewa akwai alamu Koriya ta arewa na shirin yin wasu sabbi gwajin makamai.

Kudirin Majalisar dinkin duniyar ya haramta huldar cinikayya da koriya ta arewa a abubuwan da suka jibanci makaman nukiliya da makamai masu linzami da ma kuma dukkan makamai masu guba. Bugu da kari takunkumin ya kuma shafi matsin hada hadar kudade a kan rundunar sojin kasar.

Mataki mafi tsauri shi ne na binciken shige da ficen manyan kayayyaki domin karin matsin lamba ga gwamnatin domin hana ta sayar da kayayyaki domin amfani da kudaden wajen sarrafa makamai ko sayar da makaman ga yan taádda.

Tun da farko a jawabin sa Ministan harkokin wajen kasar Japan Taro Aso ya baiyana bukatar gamaiyar kasa da kasa ta cigaba da matakan diplomasiya domin sulhunta takaddamar nukiliyar ta koriya ta arewa. A game da muhawarar da ake cewa ko ya dace Japan ita ma ta mallaki makamin nukiliya domin kare kan ta daga barazanr koriya ta arewa, Ministan harkokin wajen Japan din Taro Aso yace ko kusa Japan ba ta da shaawar mallakar makaman kare dangi. Gwajin makamin nukiliyar da koriya ta arewa ta yi ya haifar da sabon babi na yunkurin mallakar makamin kare dangi a tsakanin kasashen yankin Asia.

Ga alama fadar gwamnatin a Pyongyang bata damu da matakan diplomasiyar da Amurka ke dauka ba, da sukar lamirin da kasashen duniya ke mata ko kuma takunkumin da aka kakaba mata ba. Wata sanarwa daga maáikatar harkokin wajen kasar ta ce su kam an sha su, sun warke domin ba yau aka fara ba, sun jure makamancin wannan takunkumin wanda aka sanya musu har tsawon shekaru a baya, a saboda haka wannan ma ba zai yi wani tasiri ba.

A ranar Alhami sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice za ta wuce zuwa koriya ta kudu, kana ta nufi birnin Beijin a ranar jumaá mai zuwa. Tuni kasar China wadda take babbar abokiyar harkokin kasuwancin Koriya ta arewa ta bada goyon baya ga kudirin Majalisar duniyar.

A lardin Dandong dake kan iyaka tsakanin China da Koriya ta arewa, jamián kwastam na kasar China na binciken manyan motoci dake wucewa ta kan iyakar, sai dai baá ga wasu alamu na karin matakan tsaro ba. A gobe ne kuma idan Allah ya kai mu sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice za ta cigaba da tattaunawa da mahukuntan Japan tare da jamián Amurka a kan rawar da Japan din zata taka a farautar kayayyakin da koriya ta arewa ka iya yin fasakwaurin su domin kwace su.