1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar da Firaministan China Wen Jiabao ya kai kasar Amirka.

Mohammad Nasiru AwalDecember 10, 2003
https://p.dw.com/p/BvnC
FM Wen Jiabao na China dai ba sanya dogon buri ga tattaunawar da suka yi da shugaba GWB ba. Shugaban na Amirka dai yayi suka ga yunkurin da Taiwan ke yi na radin kanta don ballewa daga China. Kawo yanzu dai Amirka cewa ta yi ba zata taimakawa Taiwan a yunkurin da take yi na samun ´yancinta daga China ba. Shugaban Taiwan Chen Shui-bian dai ba zai yiwa kansa wani abin alheri ba, idan ya ci-gaba da yin watsi da gargadin da Amirka lke yi masa a cikin makonnin da suka wuce.

Wannan gargadin kuwa ya shafi wata kuri´ar raba gardama da shugaba Chen ke shirin gudanarwa a daidai lokacin da za´a yi zaben shugaban kasa a ran 20 ga watan maris na shekara mai zuwa. Wannan kuri´ar raba gardamar dai zata shafi barazanar da China ke yiwa Taiwan din ne. To amma babu wanda ya san manufar wannan kuri´a, watakila har da shi kanshi shugaba Chen. Muhimmin abin da ya sa gaba shine yayi amfani da kuri´ar raba gardamar don samun goyon bayan ´yan adawa, wanda hakan zai kara masa farin jini wajen sake zabensa. To sai dai hakan wani babban hadari ne ga Chen, domin yana iya rashin babbar kawarsa wato Amirka ga China.

Gwamnatin Washington ba ta da sha´awar ganin an samu wani canji a halin da ake ciki, domin tana iya tafiyar da huldodinta da dukkan bangarorin da abin ya shafa. Hakan nan ma ga China, domin ana samun ci-gaba sosai a huldodin kasuwanci da na tattalin arziki tsakanin China da Taiwan, inda a halin da ake ciki manyan kamfanonin Taiwan suka samun gindin zama a China. Saboda haka gwamnatin birnin Peking zata bi duk hanyoyin da suka wajaba don hana Taiwan samun ´yancin kai a hukumance.

Ita kuwa a nata bangaren Taiwan ba kawai wani zumunci take samu daga al´umar ta bisa manufofinta na demukiradiyya ba, a´a tana samun kariya daga Amirka a karkashin wata dokar karfafa dangantaka da Taiwan. Hakan na nufin kenan duk wani hari da China zata kaiwa Taiwan, tamkar akan Amirka ne aka kai wannan hari. Saboda haka Amirka ke taka-tsantsan tare da yiwa gwamnatin Taiwan kashedin cewa ba ita ce zata tsayar da shawara game da wani rikici da ka iya tasowa tsakanin Amirka da China ba.

Tuni dai aka manta da kalaman da shugaba Bush yayi lokacin da ya hau kan karagar mulki, inda ya kwatanta China a matsayin wata abokiyar adawa. Domin tun bayan 11 ga watan satumban shekara ta 2001 zuwa yau ake samun kyautatuwar dangantaku tsakanin manyan daulolin duniyar biyu. Gwamnatin Peking ta zama wata kawa a yakin da ake yi da ta´addanci, haka zalika ba ta nuna adawa da yakin da Washington ta yi da Iraqi ba. A rikicin da ake yi da KTA game da shirin ta na makaman nukiliya ma, China din ce ta yi ta kai gauro da mari don warware wannan rikici ta hanyar diplomasiyya.

Ita kuma China ta na bukatar taimakon Amirka musamman game da huldodin ciniki. Yanzu haka dai bayan da Amirka ta susa masa inda yake masa kaikayi game da batun Taiwan, FM China Wen yayi alkawarin kafa wani kwamitin kwararru da zai duba batun darajar takardun kudin kasar, wadda ta janyowa Amirka babban gibin ciniki da na kasafin kudi a wannan shekara.