1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Dalai Lama a Jamus

July 24, 2007

Shugaban na addinin Buddha ya zo ne halartar bikin mabiya addinin na Buddha a birin Hamburg

https://p.dw.com/p/Btuy
Dalai Lama
Dalai LamaHoto: AP

Shugaban addinin Buddha Dalai Lama yayi kira ga bin hanyoyi na kwanciyar hankali domin samarda zaman lafiya da magance dukkan kowane irin matsala a duniya,ya fadi hakan ne kuwa a ziyara kwanaki goma da ya kawo nan Jamus inda ake gudanar da babban taro na yan addin Buddha a birnin Hamburg.

Shugaban na addinin Buddha wanda ya karbi lambar yabo ta zaman lafiya a duniya yayi jawabi game da batutuwa da dama da suka shafi zaman lafiya da son juna tsakanin yan adam.

Dalai Lama yana daya daga cikin maus hankoron kare hakkin bil adama a duniya musamman ganin yadda kasar china ke cin zarafin jama’ar Tibeti.Yace har yanzu matsalar take hakkin bil adama na nan a yankin Tibet.

„yancin dan adam har yanzu matsala ce babba,kamar wata guda daya wuce na sadu da wani dan Tibeti wanda yayi zaman shekaru 8 a gidan yari na China,ya kuma ce laifinsa shine don ya fadi albarkacin bakinsa,wanda kowa yake da yancin yin hakan amma a Tibeti abin ya sha bambam“

ya kuma fadawa manema labari cewa bai ji dadain yajin kin cin abinci da daliban Tibeti a China sukayi ba game da halinda jamaarsu ke ciki amma yace ya fahimci irin bakin cikinsu ganin cewa babu wani ci gaba a halin rayuwar jamaar Tibet.

Game da ko yana ganin goyon baya da yanzu yake samu daga jamus ya isa ko kuwa akwai abinda suke bukata Dalai Lama yace:

„gwamnatin Jamus kamar sauran gwamnatoci tana tausaya mana kuma ta nuna damuwarta akanmu,nuna irin wannan damuwa daga kasashen ketare abu ne da muke godiya dashi kuma muke bukata,duk da cewa babu wata alama ta kawo karshen matsalolinmu“

Shugaban na addinin Buddha na duniya yace fafutuka da yake yi na zaman lafiya da kare yanci ba ga jamaar tibeti kadai yakeyiba.

„na ziyarci kasashe da dama,babban abinda na sanya a gaba ba batun Tibeti bane kadai,muhimmi shine kare mutuncin dan adam,ina son ganin kowa cikin farin ciki da walwala,saboda haka ian ganin cewa duk wani dan adama yana da yacin kasancewa cikin yanci da walwala“

Shugaban na Buddha yace yana da shaawar zama cikin alummarsa amma kuma aiyukan da ya sanya a gaba ba zasu bashi damar yin hakan ba.

„sosai kwari kuwa babu wanda baya son komawa gida,amma ni yanzu a matsayina na sufi na addinin Buddha babu dama,domin kuwa da zarar mutum ya zama sufi ya yanke hulda ke nan da iyalinsa“

A makon daya gabata dai kasar China ta zargi Dalai Lama da kokarin raba kann Tibeti ta kuma gargadi Jamus da kada ta bashi damar yada abinda ta kira akidarsa ta aware.