1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Egeland a Zimbabwe

Ibrahim SaniDecember 5, 2005

Ko shin yaya ziyarar Egeland take kasancewa a kasar Zimbabwe..

https://p.dw.com/p/Bu3f
Jan Egeland
Jan EgelandHoto: AP

Rahotanni dai da suka iso mana daga wannan kasa ta Zimbabwe na nuni da cewa Shugaban hukumar bada tallafin na Mdd, wato Jan Egelan ya nuna bacin ransa ne game da hali na matsi da fatara da alummar yankunan da aka rushewa gidajen kwana da guraren sana´oin su ke ciki.

Shugaban ya kara da cewa wannan ziyara ta kuma tabbatar min da karancin muhalli da yawa yawan alummomin wadan nan gurare ke ciki, a sakamakon rurrushe musu gidajen kwana da akayi.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa Jan Egeland ya furta hakan ne a sakamakon ziyar gani da ido daya kai izuwa guraren da gwamnatin kasar ta Zimbabbwe ta Rurrushe a watan mayu daya gabata.

Bayanai dai daga kasar sun shaidar da cewa a tun lokacin da gwamnatin kasar ta Gudanar da wadannan rushe rushe, dubbannin mutane na guraren da abun ya shafa ke cikin halin kaka ni kayi na rashin gurin kwana da kuma guraren gudanar da sana´oin su.

Bugu da kari bayanan sun kuma tabbatar da barkewar cututtuka irin su gudawa da dangogin su a sakamakon gurbatar muhalli na dagwalo da shara gada yawa daga cikin mutanen da wannan abu ya shafa.

A cewar hukumar ta Mdd, a yanzu haka akwai mutane kusan dubu dari bakwai da basu da guraren kwana ko kuma guraren gudanar da sana´oin su a sakamakon wannan rushe rushe sannan a hannu daya kuma akwai mutane a kalla miliyan biyu da digo hudu da kusan wadan nan matsaloli biyu da muka ambata a sama ta shafa.

Game kuwa da wannan hali da ake ciki tuni gwamnatin ta Mugabe tace ta shirya giggina wasu sabbin gidaje don bawa wadanda wannan abu ya shafa,to amma a maimakon fara gina gidajen sai gwamnati ta aiwatar da wannan shiri, wanda hakan yanzu ya haifar da mawuyacin hali ga dubbannin mutanen kasar.

Rahotanni dai sun tabbatarr da cewa kafin kai wannan ziyara izuwa wadan nan gurare da rushe rushen ya shafa, a jiya lahadi sai da Egeland ya gana da jami´in hukumar ta Mdd dake kasar ta Zimbabwe don sanin ainihin halin da ake ciki a kasar ta Zimbabwe.

A kuma gobe talata ne ake sa ran shugaban hukumar kula da bayar da tallafin na Mdd aka shirya cewa zai gana da Shugaba Robert Mugabe.

A yanzu haka dai gamsassun bayanai daga kasar na nuni da cewa kasar ta Zimbabwe na cikin wani mawuyacin hali na tattalin arziki da kuma siyasa, sannan a hannu daya kuma ga matsalar rashin wadatar abinci a kasar, koda yake gwamnatin ta Bugabe ta ta´allaka matsalar abincin da matsalar fari da kasar ta fuskanta.