1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Gates a Afganistan

September 2, 2010

Sakataren tsaron Amirka na ziyarar ba-zata a Afganistan.

https://p.dw.com/p/P2fF
Robert Gates, sakataren tsaron Amirka.Hoto: AP

Sakataran tsaro na Amirka Robert Gates ya fara wata ziyarar aiki ta ba-zata a yau a Afganistan bayan wadda ya kammala a ƙasar Iraƙi, inda ya bayyana kawo ƙarshen kai hare-haren dakarun AmIrka a yaƙin da gwamnatin ƙasar ta ke yi da 'yan ƙungiyar Taliban. Ziyarar ta Gates wacce ta zo a daidai lokacin da dakarun Amirkan da ke da yawan kashi biyu cikin ukku na dakarun ƙasashen duniya kimanin dubu 150 a Afganistan na yin bita akan irin mumunar asarar rayukan jama'a da suka samu a tsawon watannin tara na yaƙin da suka gwabza da ƙungiyar Taliban. An shirya dai sakataren tsaron na Amirka zai gana da Shugaba Hamid Karzai a birnin Kabul da kuma babban kwamandan dakarun ƙawance na ƙasa da ƙasa Janar David Petraeus.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas