1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Hamas a kasar Saudiya

March 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5M

Shugabannin kungiyar Hamas sun isa kasar Saudiyya a wata ziya ta neman goyon baya ta fuskar siyasa da tallafin kudi ga gwamnatin Palasdinawa. Kasar Saudiyya wadda ta ke daula ta musulunci kuma mai arzikin mai a duniya na daya daga cikin kasashe dake tallafawa hukumar gudanarwar Palasdinawa. Hamas ta shiga ziyarar kasashen larabawa da sauran kasashe na duniya. A yanzu Hamas din wadda ta sami nasara a zaben majalisun dokoki na yankin Palasdinawa na kokari ne domin kafa sabuwar gwamnati. Amurka da kungiyar tarayyar turai sun yi barazanar dakatar da gudunmawar jin kai ga hukumar Palasdinawa, har sai Hamas ta ajiye makan ta, ta kuma amince da wanzuwar kasar Israila. Ministan harkokin wajen saudiyyan Saud al-Faisal ya soki lamirin kasashen duniya na maida Hamas saniyar ware.